lallai Labarin da muka samu yanzunnan na nuna cewa Allah ya yiwa tsohon gwamnan jihar Kano kuma tsohon ministan birnin tarayya, AVM Hamza Abdullahi rasuwa. Tsohon sojan ya rasu ne a kasar Jamus ranan Laraba, 2 ga watan Junairu, 2018. AVM Hamza Abdullahi ya kasance gwamnan mulkin soja ne tsakanin shekarar 1984 da 1985 yayinda shugaba Muhammadu Buhari ke mulkin kasar Nigeriarmu.
No comments:
Post a Comment