Tuesday, 1 January 2019

TABBAS NA CIKA DUKKAN ALKAWURRAN DANA DAUKA A ZABEN 2015 DA YA GABATA

Fadar Buhari, al’ummar Najeriya ba za su yi nadamar kada kuri’unsu ga ‘yan takarar jami’yyar APC a zaben 2019 da ke tafe ba. Shugaban ya ce, ya cika alkawuransa a bangarorin da suka shafi tsaro da tattalin arziki da kuma yaki da cin hanci da rashawa, yayin da ya jaddada aniyarsa ta ci gaba da sa kafar wando daya da masu wawure dukiyar talakawa muddin ya koma kan karagar mulki. Koda yake Buharin ya ce, yaki da mayakan Boko Haram na ci gaba da zama kalubale a wasu sassan kasar, amma za a kawar da matsalar tsaron da kungiyar ke haifarwa a kasar. Har ila yau, Buhari ya ce, matsalar rashin aikin yi na ci gaba da addabar kasar, amma gwamnatin na kokarin shawo kanta. A bangaren harkar noma kuwa, shugaba Buhari ya ce, gwamnatinsa ta karfafa guiwar manoma don tabbatar da tsaron abinci a fadin kasar  baki daya.

No comments:

Post a Comment