Thursday, 3 January 2019

SABANIN RA.AYIN 'YAN FINAFINAI AKAN SHUWAGABANCIN NAJERIYA

Ta yayin da siyasa ke cigaba da mamaya da ratsa jiki da harkokin jama'a, an yi sharhi a kan yadda goyon bayan Atiku da Buhari ya raba kan jaruman Kannywood

- Yin sharhin ya biyo bayan ganin yadda jaruman ke fitowa fili domin nuna goyon bayansu ga dan takarar da su ke ra'ayi

- Sai dai har yanzu ba a san ina wasu fitattun jarumai irin su Ali Nuhu, Sadiq Sani Sadiq, Rahama Sadu, Hadiza Gabon da Nafisa Abdullahi su ka saka gaba ba

Masana'antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood ta bawa shugaba Buhari muhimmiyar gudunmawa wajen samun nasara a zaben shekarar 2015.

Jaruman fina-finan Hausa da mawaka sun sha halartar taron jam'iyyar APC da yakin zaben Buhari domin nuna goyon bayansu. Kazalika mawaka sun rera ma sa wakoki.
[1/3, 4:22 PM] yearqub: akasarin jaruman sun kasance suna goyon bayan buhari sai dai yanzu fitowar Atiku a PDP ta janye wasu jaruman fina-finan.

Daga cikin jaruman Kannywood da har yanzu ke tare da Buhari akwai;

1. Adam A. Zango

2. Nura Hussain

3. Yusuf Haruna (Baban Chinedu)

4. Jamila Nagudu

5. Halima Atete

6. Rukayya Dawayya

7. Bello Muhammad Bello (BMB)

8. Dauda Kahutu Rarara (Mawaki)

DUBA WANNAN: Jerin sunayen jaruman Kannywood 12 da ke yiwa Atiku kamfen

9. Nazifi Asnanic (Mawaki)

10. El-Mu'az Birniwa (Mawaki)

11. Fati Nijar (Mawakiya)

12. Mawaki Aminu Ladan (ALA)

13. Hussaini Danko (Mawaki)

14. Fati Shu'uma

15. Rabi'u Rikadawa

Ragowar jarumar fim din Hausa irinsu Ali Nuhu, Rahama Sadau, Hadiza, Sadiq Sani Sadiq, Nafisa Abdullahi, da sauransu ba su bayyana dan takarar da su ke goyon baya ba.


No comments:

Post a Comment