Sunday, 6 January 2019

AISHA BUHARI TAYI MAGANA AKAN GANDUJE A TARONTA NA KANO

   
   Uwar gidan shugaban kasar Najeriya Aisha Buhari a ranar Asabar din da ta gabata wajen taron da ta gudanar a jihar Kano ta kunyata Gwamnan jihar Dakta Abdullahi Umar Ganduje lokacin da ta tashi tayi tafiyar ta yana tsakar yin jawabin sa wajen taron. Kamar dai yadda muka samu, uwar gidan shugaban kasar ta gudanar da wani taro ne ta kungiyar ta ta yakin neman sake zaben mijin ta karo na biyu da ta kunshi mata da matasa tare da kaddamar da shugabannin ta a jihar.
     
      Kamar dai yadda jaridar DailyNigerian ta ruwaito, wannan ya sabawa al'ada kuma hakan bai rasa nasaba da irin yadda ba'a tsara jadawalin taron ba yadda ya kamata wanda hakan bai yi wa uwargidan shugaban kasar dadi ba.

No comments:

Post a Comment