Dan kwallon tawagar Juventus bai lashe kyautar hukumar kwallon kafa ta duniya da ta Turai UEFA ba, wadda dan wasan Real Madrid, Luka Modric ya karbe a 2018.
Ronaldo ya ce ya fi mayar da hankali kan nasarar kungiya, ba wai ta kashin kansa shi kadai ba, domin kwallon kafa ba ta mutun daya ba ce.
[1/1, 10:27 AM] yearqub: Haka kuma dan wasan na Portugal bai lashe kyautar dan wasan da ya taka rawa a gasar kofin duniya da aka yi a Rasha ba, ita ma Modric ne zakara.
Ronaldo ya lashe kofin Zakaraun Turai tare da Real Madrid, bayan da ta yi nasara a kan Liverpool da ci 3-1 a ranar 26 ga watan Mayun 2018.
Juventus tana ta daya a kan teburin Serie A, sannan ta kai zagaye na biyu a gasar cin kofin Zakarun Turai ta Champions League.
Haka kuma tawagar kwallon kafar Portugal ta kai wasan daf da karshe a Nations League, inda za ta fafata da Switzerland a cikin watan Yunin 2019 inda muka dosa.
No comments:
Post a Comment