Sunday, 6 January 2019

AN KONA SHAGUNA DA GIDAJE A IBADAN


 Wasu batagari daga wasu sassan garin Ibadan, babban birnin jihar Oyo, sun saka wa gidaje fiye da 20 wuta a wani rikici tsakanin kungiyoyin 'yan daba a yankin Idi Arera. Daga cikin gine-ginen da 'yan dabar suka saka wa wutar akwai shagunan masu dinki, shagunan sayar da lemukan roba, shagunan kayan wutar lantarki da na abinci da na kayan sawa da sauran su. Majiyar ta shaida mata cewar barkewar rikicin na safiyar yau, Lahadi, ya biyo bayan rigingimun dake faruwa ne tsakanin kungiyoyin 'yan dabar. Rahotanni sun bayyana cewar ba don dagewar 'yan kungiyar bijilanti da wasu jama'ar unguwa ba yayin rikicin, da barnar da 'yan dabar zasu yi sai ta fi haka. A wani labarin na daga jihar ta Oyo, kun ji cewar Tsohon Sanata kuma tsohon gwamnan jihar, Rashidi Ladoja, ya ce ya yi ritaya daga yin takarar kowacce kujera a Najeriya saboda wahalar da ya ce ya sha lokacin da yake gwamna.

 sun kona gidaje da shaguna a sabon rikicin da ya barke a Ibadan  mai rike da mukamin Olubadan na kasar Ibadan, ya zama gwamna a jihar Oyo a tsakanin shekarar 2003 zuwa shekarar 2007 a karkashin jam'iyyar PDP. an tsige shi a watan Janairu na shekarar 2006, amma kotu ta mayar da shi a shekarar a watan Disamba na shekarar.
 
   koda yake wannan kalami a yau, Asabar, Ladoja ya bayyana cewar ya yanke shawarar yin bankwana da takara ne saboda samun lokacin kulawa da bukatun iyalinsa. A hirar sa da manema labarai a garin Igholo, hedkwatar karamar hukumar Oorelope, Ladoja ya ce, "kadan ya rage na manta da iyalina lokacin da nake gwamnati. Mun yi iya bakin kokarinmu, amma ni kam ba zan kara yin takara ba.

No comments:

Post a Comment