Tuesday, 1 January 2019

LIONEL MESSI YA LASHE TAKALMIN ZINARE NA BIYAR

Hakika Dan wasan Barcelona, Leo Messi ya lashe kyautar takalmin zinare karo na biyar a ranar Talata a matsayin wanda ya fi cin kwallo a kakar bara.

Kyaftin din tawagar Argentina wanda ya fi kowa lashe kyautar a tarihi, ya ci kwallo 34 a wasa 36 da ya yi a gasar La Ligar Spaniya a kakar 2017/18.

An gudanar da bikin bai wa Messi kyautar a Antiga Fàbrica Estrella Damm da ke birnin Barcelona, inda shugaban kungiyar Josep Maria Bartomeu ya halarta.

Wasu da suka halarci bikin sun hada da Pep Segura da Éric Abidal da Guillermo Amor da Ramon Planes da Jordi Roura da Aureli Altimira da Sergio Busquets da kuma Sergi Roberto.

Ga lokutan da Messi ya lashe kyautar a baya

    2009/10 - Kwallo 34
    2011/12 - Kwallo 50
    2012/13 - Kwallo 46
    2016/17 - Kwallo 37
    2017/18 - Kwallo 34

Abokin wasan Messi Luis Suárez ya taba cin takalmin zinaren sau biyu, wanda ya fara dauka a shekarar 2013/14 a lokacin da ya ke Liverpool, sannan ya lashe a kakar 2015/16.

Messi shi ne kan gaba a nahiyar Turai a yawan cin kwallo a kakar da muke ciki, inda ya zura kwallaye 14 a raga ras.

No comments:

Post a Comment