Wednesday, 2 January 2019

KUNGIYAR KIRITOCIN AREWA TACE BUHARI BAZAI SAKE LASHE ZABEN WANNAN SHEKARA BA TA 2019

Lallai Kungiyar kiristocin Arewa sunyi kira ga 'yan Najeriya kada su zabi shugaba Muhammadu Buhari a zaben 2019 - Kungiyar ta ce shugaba Buhari ya gaza cika alkawurran da ya dauka wa 'yan Najeriya a yayin yakin neman zabe - Kungiyar ta ce ba a taba samun gwamnati mai muni kamar gwamnatin Buhari ba tun kafa Najeriya tare da lissafo matsalolin tsaro da suka dabaibaye kasar Kungiyar mabiya addinin kirista na Arewa 'Arewa Christians and Indigenous Pastors Association' (ACIPA) tayi kira ga 'yan Najeriya su nemi wani dan takarar shugabancin kasa bayan Shugaba Muhammadu Buhari saboda shi ba alheri bane ga kasar. A sakon sabuwar shekarar da kungiyar da fitar mai dauke da sa hannun shugaban ta Rabaran Luka Shehu, kungiyar ta ce shekarun da gwamnatin Buhari ta kwashe tana mulki sune mafi muni a tarihin Najeriya.
[1/2, 12:26 AM] yearqub: Sanarwar ta ce: "A yayin da muke sa ran samun cigaba da tsaro a Najeriya a shekarar 2019 da shekarun da za su biyo baya, yana da kyau mu lura da yadda gwamnatin shugaba Buhari ta gaza cika alkawurran da ta yiwa 'yan Najeriya tun 2015. "An samun karin rashin jituwa tsakanin kirista da sauran mabiya addinai, kashe-kashen mikiyaya ya karu kuma ana cigaba da yiwa mabiya addinin kirista kisan kiyashi. Sace 'yan matan Dapchi da rashin karbo Leah Sharibu daga hannun 'yan ta'adda da kuma hare-haren da 'yan ta'adda ke kaiwa a Metele, Baga da sauran garuruwa da kuma kashe-kashen jihar Kaduna, Yobe, Plateau da jihohin Zamfara inda ake sace sarakuna ana kashe su duk alamomi ne da ke nuna gwamnatin Buhari ta gaza." Kungiyar ta ce a garuruwan da ake mutunta mutane, shugaban kasa da shugabanin hukumomin tsaro kamata ya yi suyi murabus saboda sun gaza wurin gudanar da aikin su na kiyaye rayuka da dukiyoyin al'umma gabadaya.

No comments:

Post a Comment