Wednesday, 2 January 2019

KUNGIYAR KIRISTOCI TA BAUCHI

ilahirin Kungiyar Matasa Kiristoci ta Bauchi ta janye daga batun marawa gwamna baya kan tazarce Source: UGC Kungiyar matasan kiristoci ta kasa reshen jihar Bauchi ta wanke kanta daga rahoton cewa kungiyar kiristoci ta kasa akan cewa suna goyon bayan sake zaben gwamnan jihar, Mohammed Abdullahi Abubakar. A wata takardar da kakakin kungiyar yasa hannu, Comrade Daure David Yankoli ya bawa manema labarai a ranar lahadi, 30 ga watan Disamba,2018 cewa kungiyar ta wanke kanta daga goyon bayan gwamnan wanda Rev Joshua Ray Maina, shugaban kungiyar a ziyarar kirsimati da suka kai gidan gwamnatin jihar. Takardar ta kunshi, "An jawo hankalin kungiyar matasan kiristoci da kafar watsa labarai ta CAN ta sanar da cewa kungiyar tana goyon bayan kara zaben gwamnan jihar a zaben 2019 mai zuwa." Kakakin kungiyar ya kushe tare da wanke kansu daga wannan batu domin kungiyar su ba ta siyasa ce ba.

No comments:

Post a Comment