Shi Marigayi Shehu Shagari ya rasu ne a ranar Juma'a a 28 ga watan Disamba a wani asibiti da ke babban birnin tarayya Abuja yana da shekaru 93. An binne shi ne kuma a wani kangon daki da ke wani sashen na gidansa da ke garin Shagari ranar Assabar. Mutane da dama sun yi tsammanin za a binne shi ne a Hubbaren Shehu inda kabarin Sheikh Usmanu Danfodiyo da na yawancin sarakunan daular Usmaniyya suke ciki.
No comments:
Post a Comment