Sunday, 6 January 2019
AISHA BUHARI TAYI MAGANA AKAN GANDUJE A TARONTA NA KANO
Uwar gidan shugaban kasar Najeriya Aisha Buhari a ranar Asabar din da ta gabata wajen taron da ta gudanar a jihar Kano ta kunyata Gwamnan jihar Dakta Abdullahi Umar Ganduje lokacin da ta tashi tayi tafiyar ta yana tsakar yin jawabin sa wajen taron. Kamar dai yadda muka samu, uwar gidan shugaban kasar ta gudanar da wani taro ne ta kungiyar ta ta yakin neman sake zaben mijin ta karo na biyu da ta kunshi mata da matasa tare da kaddamar da shugabannin ta a jihar.
Kamar dai yadda jaridar DailyNigerian ta ruwaito, wannan ya sabawa al'ada kuma hakan bai rasa nasaba da irin yadda ba'a tsara jadawalin taron ba yadda ya kamata wanda hakan bai yi wa uwargidan shugaban kasar dadi ba.
AN KONA SHAGUNA DA GIDAJE A IBADAN
Wasu batagari daga wasu sassan garin Ibadan, babban birnin jihar Oyo, sun saka wa gidaje fiye da 20 wuta a wani rikici tsakanin kungiyoyin 'yan daba a yankin Idi Arera. Daga cikin gine-ginen da 'yan dabar suka saka wa wutar akwai shagunan masu dinki, shagunan sayar da lemukan roba, shagunan kayan wutar lantarki da na abinci da na kayan sawa da sauran su. Majiyar ta shaida mata cewar barkewar rikicin na safiyar yau, Lahadi, ya biyo bayan rigingimun dake faruwa ne tsakanin kungiyoyin 'yan dabar. Rahotanni sun bayyana cewar ba don dagewar 'yan kungiyar bijilanti da wasu jama'ar unguwa ba yayin rikicin, da barnar da 'yan dabar zasu yi sai ta fi haka. A wani labarin na daga jihar ta Oyo, kun ji cewar Tsohon Sanata kuma tsohon gwamnan jihar, Rashidi Ladoja, ya ce ya yi ritaya daga yin takarar kowacce kujera a Najeriya saboda wahalar da ya ce ya sha lokacin da yake gwamna.
sun kona gidaje da shaguna a sabon rikicin da ya barke a Ibadan mai rike da mukamin Olubadan na kasar Ibadan, ya zama gwamna a jihar Oyo a tsakanin shekarar 2003 zuwa shekarar 2007 a karkashin jam'iyyar PDP. an tsige shi a watan Janairu na shekarar 2006, amma kotu ta mayar da shi a shekarar a watan Disamba na shekarar.
koda yake wannan kalami a yau, Asabar, Ladoja ya bayyana cewar ya yanke shawarar yin bankwana da takara ne saboda samun lokacin kulawa da bukatun iyalinsa. A hirar sa da manema labarai a garin Igholo, hedkwatar karamar hukumar Oorelope, Ladoja ya ce, "kadan ya rage na manta da iyalina lokacin da nake gwamnati. Mun yi iya bakin kokarinmu, amma ni kam ba zan kara yin takara ba.
Thursday, 3 January 2019
FADAR JARUMAR HAUSA FILM MAI SUNA NAFISA ABDULLAHI AKAN ADAM A ZANGO
Hakika Shahararriyar jarumar na ta masana’antar shirya fina-finan Hausa wato Kannywood Nafisa Abdullahi ta bayyana matsayar soyayyarta da jarumi Adam A. Zango, a cewarta a baya sun yi soyayya da shi, sai dai yanzu mutunci ne kawai tsakaninsu, amma ba soyayya ba. A shekarun baya an yi tunanin Nafisa Abdullahi da Adam za su yi aure duba ga yadda suka fito karara suka nuna suna matukar kaunar juna.
to Amma Jarumar ta ce yanzu tsawon shekara biyar ba su tare. Ta ce kamar yadda Allah Ya hada su kuma Ya raba. Nafisa ta ce: "Ba sai na fito na fara bayanin an yi kaza ko kaza ba, zama ne ya zo karshe muka rabu," in ji Nafisa bayan an tambaye ta dalilin rabuwarsu. "A baya mun fi ayyuka tare kuma an fi ganinmu tare amma yanzu ba mu cika haduwa da juna ba sosai saboda ban cika fitowa a fina-finai ba.
ita Jarumar ta ce yanzu ta dauki Zango a matsayin abokin aiki amma ba soyayya tsakaninsu. Ta ce ba su cika haduwa da shi ba a yanzu. "Ba mu da wata matsala ta rashin jituwa da juna tsakani na da shi.
SABANIN RA.AYIN 'YAN FINAFINAI AKAN SHUWAGABANCIN NAJERIYA
Ta yayin da siyasa ke cigaba da mamaya da ratsa jiki da harkokin jama'a, an yi sharhi a kan yadda goyon bayan Atiku da Buhari ya raba kan jaruman Kannywood
- Yin sharhin ya biyo bayan ganin yadda jaruman ke fitowa fili domin nuna goyon bayansu ga dan takarar da su ke ra'ayi
- Sai dai har yanzu ba a san ina wasu fitattun jarumai irin su Ali Nuhu, Sadiq Sani Sadiq, Rahama Sadu, Hadiza Gabon da Nafisa Abdullahi su ka saka gaba ba
Masana'antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood ta bawa shugaba Buhari muhimmiyar gudunmawa wajen samun nasara a zaben shekarar 2015.
Jaruman fina-finan Hausa da mawaka sun sha halartar taron jam'iyyar APC da yakin zaben Buhari domin nuna goyon bayansu. Kazalika mawaka sun rera ma sa wakoki.
[1/3, 4:22 PM] yearqub: akasarin jaruman sun kasance suna goyon bayan buhari sai dai yanzu fitowar Atiku a PDP ta janye wasu jaruman fina-finan.
Daga cikin jaruman Kannywood da har yanzu ke tare da Buhari akwai;
1. Adam A. Zango
2. Nura Hussain
3. Yusuf Haruna (Baban Chinedu)
4. Jamila Nagudu
5. Halima Atete
6. Rukayya Dawayya
7. Bello Muhammad Bello (BMB)
8. Dauda Kahutu Rarara (Mawaki)
DUBA WANNAN: Jerin sunayen jaruman Kannywood 12 da ke yiwa Atiku kamfen
9. Nazifi Asnanic (Mawaki)
10. El-Mu'az Birniwa (Mawaki)
11. Fati Nijar (Mawakiya)
12. Mawaki Aminu Ladan (ALA)
13. Hussaini Danko (Mawaki)
14. Fati Shu'uma
15. Rabi'u Rikadawa
Ragowar jarumar fim din Hausa irinsu Ali Nuhu, Rahama Sadau, Hadiza, Sadiq Sani Sadiq, Nafisa Abdullahi, da sauransu ba su bayyana dan takarar da su ke goyon baya ba.
CEWAR DAN WASAN REAL MADRID MAI SUNA ISCO
Hakika Dan wasan Real Madrid wato Isco yace bazai bar kungiyar a wasannan kakar wasannin ba, Dan wasan dai ana alakantashi da komawa kungiyar kwallon kafa ta Chelsea dake kasar England.
Manchester City suna neman dan wasan Real Betis mai suna Junior Firpo dan asalin kasar Spain mai shekaru 22.
Dan wasan Liverpool wato Solanke yana Crystal Palace ana gwajin lafiyarsa biyo bayan cimma yarjejeniya da Liverpool tayi da Crystal Palace kan daukan dan wasan a matsayi na aro zuwa gaba.
ANTANTANCE HIJIRAN DAN WASAN B/DORMOUND MAI SUNA PULISIC
antantance dan wasan Dortmund wato Pulisic zai koma Chelsea ne ba Liverpool ba kamar yadda ake ta rade-radi.
Dan wasan da Barcelona, Manchester City da kuma Arsenal suke neman wato Nicolas Pepe ya shaidawa kungiyarsa ta Lille dake kasar France cewar shifa yanaso ya tafi.
TSOHON GWAMNAN KANO MAI SUNA AVM HAMZA ABDULLAHI YA RASU
lallai Labarin da muka samu yanzunnan na nuna cewa Allah ya yiwa tsohon gwamnan jihar Kano kuma tsohon ministan birnin tarayya, AVM Hamza Abdullahi rasuwa. Tsohon sojan ya rasu ne a kasar Jamus ranan Laraba, 2 ga watan Junairu, 2018. AVM Hamza Abdullahi ya kasance gwamnan mulkin soja ne tsakanin shekarar 1984 da 1985 yayinda shugaba Muhammadu Buhari ke mulkin kasar Nigeriarmu.
Wednesday, 2 January 2019
KUNGIYAR KIRISTOCI TA BAUCHI
ilahirin Kungiyar Matasa Kiristoci ta Bauchi ta janye daga batun marawa gwamna baya kan tazarce Source: UGC Kungiyar matasan kiristoci ta kasa reshen jihar Bauchi ta wanke kanta daga rahoton cewa kungiyar kiristoci ta kasa akan cewa suna goyon bayan sake zaben gwamnan jihar, Mohammed Abdullahi Abubakar. A wata takardar da kakakin kungiyar yasa hannu, Comrade Daure David Yankoli ya bawa manema labarai a ranar lahadi, 30 ga watan Disamba,2018 cewa kungiyar ta wanke kanta daga goyon bayan gwamnan wanda Rev Joshua Ray Maina, shugaban kungiyar a ziyarar kirsimati da suka kai gidan gwamnatin jihar. Takardar ta kunshi, "An jawo hankalin kungiyar matasan kiristoci da kafar watsa labarai ta CAN ta sanar da cewa kungiyar tana goyon bayan kara zaben gwamnan jihar a zaben 2019 mai zuwa." Kakakin kungiyar ya kushe tare da wanke kansu daga wannan batu domin kungiyar su ba ta siyasa ce ba.
KUNGIYAR KIRITOCIN AREWA TACE BUHARI BAZAI SAKE LASHE ZABEN WANNAN SHEKARA BA TA 2019
Lallai Kungiyar kiristocin Arewa sunyi kira ga 'yan Najeriya kada su zabi shugaba Muhammadu Buhari a zaben 2019 - Kungiyar ta ce shugaba Buhari ya gaza cika alkawurran da ya dauka wa 'yan Najeriya a yayin yakin neman zabe - Kungiyar ta ce ba a taba samun gwamnati mai muni kamar gwamnatin Buhari ba tun kafa Najeriya tare da lissafo matsalolin tsaro da suka dabaibaye kasar Kungiyar mabiya addinin kirista na Arewa 'Arewa Christians and Indigenous Pastors Association' (ACIPA) tayi kira ga 'yan Najeriya su nemi wani dan takarar shugabancin kasa bayan Shugaba Muhammadu Buhari saboda shi ba alheri bane ga kasar. A sakon sabuwar shekarar da kungiyar da fitar mai dauke da sa hannun shugaban ta Rabaran Luka Shehu, kungiyar ta ce shekarun da gwamnatin Buhari ta kwashe tana mulki sune mafi muni a tarihin Najeriya.
[1/2, 12:26 AM] yearqub: Sanarwar ta ce: "A yayin da muke sa ran samun cigaba da tsaro a Najeriya a shekarar 2019 da shekarun da za su biyo baya, yana da kyau mu lura da yadda gwamnatin shugaba Buhari ta gaza cika alkawurran da ta yiwa 'yan Najeriya tun 2015. "An samun karin rashin jituwa tsakanin kirista da sauran mabiya addinai, kashe-kashen mikiyaya ya karu kuma ana cigaba da yiwa mabiya addinin kirista kisan kiyashi. Sace 'yan matan Dapchi da rashin karbo Leah Sharibu daga hannun 'yan ta'adda da kuma hare-haren da 'yan ta'adda ke kaiwa a Metele, Baga da sauran garuruwa da kuma kashe-kashen jihar Kaduna, Yobe, Plateau da jihohin Zamfara inda ake sace sarakuna ana kashe su duk alamomi ne da ke nuna gwamnatin Buhari ta gaza." Kungiyar ta ce a garuruwan da ake mutunta mutane, shugaban kasa da shugabanin hukumomin tsaro kamata ya yi suyi murabus saboda sun gaza wurin gudanar da aikin su na kiyaye rayuka da dukiyoyin al'umma gabadaya.
[1/2, 12:26 AM] yearqub: Sanarwar ta ce: "A yayin da muke sa ran samun cigaba da tsaro a Najeriya a shekarar 2019 da shekarun da za su biyo baya, yana da kyau mu lura da yadda gwamnatin shugaba Buhari ta gaza cika alkawurran da ta yiwa 'yan Najeriya tun 2015. "An samun karin rashin jituwa tsakanin kirista da sauran mabiya addinai, kashe-kashen mikiyaya ya karu kuma ana cigaba da yiwa mabiya addinin kirista kisan kiyashi. Sace 'yan matan Dapchi da rashin karbo Leah Sharibu daga hannun 'yan ta'adda da kuma hare-haren da 'yan ta'adda ke kaiwa a Metele, Baga da sauran garuruwa da kuma kashe-kashen jihar Kaduna, Yobe, Plateau da jihohin Zamfara inda ake sace sarakuna ana kashe su duk alamomi ne da ke nuna gwamnatin Buhari ta gaza." Kungiyar ta ce a garuruwan da ake mutunta mutane, shugaban kasa da shugabanin hukumomin tsaro kamata ya yi suyi murabus saboda sun gaza wurin gudanar da aikin su na kiyaye rayuka da dukiyoyin al'umma gabadaya.
Tuesday, 1 January 2019
LIONEL MESSI YA LASHE TAKALMIN ZINARE NA BIYAR
Hakika Dan wasan Barcelona, Leo Messi ya lashe kyautar takalmin zinare karo na biyar a ranar Talata a matsayin wanda ya fi cin kwallo a kakar bara.
Kyaftin din tawagar Argentina wanda ya fi kowa lashe kyautar a tarihi, ya ci kwallo 34 a wasa 36 da ya yi a gasar La Ligar Spaniya a kakar 2017/18.
An gudanar da bikin bai wa Messi kyautar a Antiga Fàbrica Estrella Damm da ke birnin Barcelona, inda shugaban kungiyar Josep Maria Bartomeu ya halarta.
Wasu da suka halarci bikin sun hada da Pep Segura da Éric Abidal da Guillermo Amor da Ramon Planes da Jordi Roura da Aureli Altimira da Sergio Busquets da kuma Sergi Roberto.
Ga lokutan da Messi ya lashe kyautar a baya
2009/10 - Kwallo 34
2011/12 - Kwallo 50
2012/13 - Kwallo 46
2016/17 - Kwallo 37
2017/18 - Kwallo 34
Abokin wasan Messi Luis Suárez ya taba cin takalmin zinaren sau biyu, wanda ya fara dauka a shekarar 2013/14 a lokacin da ya ke Liverpool, sannan ya lashe a kakar 2015/16.
Messi shi ne kan gaba a nahiyar Turai a yawan cin kwallo a kakar da muke ciki, inda ya zura kwallaye 14 a raga ras.
Kyaftin din tawagar Argentina wanda ya fi kowa lashe kyautar a tarihi, ya ci kwallo 34 a wasa 36 da ya yi a gasar La Ligar Spaniya a kakar 2017/18.
An gudanar da bikin bai wa Messi kyautar a Antiga Fàbrica Estrella Damm da ke birnin Barcelona, inda shugaban kungiyar Josep Maria Bartomeu ya halarta.
Wasu da suka halarci bikin sun hada da Pep Segura da Éric Abidal da Guillermo Amor da Ramon Planes da Jordi Roura da Aureli Altimira da Sergio Busquets da kuma Sergi Roberto.
Ga lokutan da Messi ya lashe kyautar a baya
2009/10 - Kwallo 34
2011/12 - Kwallo 50
2012/13 - Kwallo 46
2016/17 - Kwallo 37
2017/18 - Kwallo 34
Abokin wasan Messi Luis Suárez ya taba cin takalmin zinaren sau biyu, wanda ya fara dauka a shekarar 2013/14 a lokacin da ya ke Liverpool, sannan ya lashe a kakar 2015/16.
Messi shi ne kan gaba a nahiyar Turai a yawan cin kwallo a kakar da muke ciki, inda ya zura kwallaye 14 a raga ras.
CRISTIANO RONALDO YACE BAI DAMU BA DA CIN KOFIN KWALLON KAFA WATO 'league' BAYAN YA LACE BALLON'D'OR BIYAR
Dan kwallon tawagar Juventus bai lashe kyautar hukumar kwallon kafa ta duniya da ta Turai UEFA ba, wadda dan wasan Real Madrid, Luka Modric ya karbe a 2018.
Ronaldo ya ce ya fi mayar da hankali kan nasarar kungiya, ba wai ta kashin kansa shi kadai ba, domin kwallon kafa ba ta mutun daya ba ce.
[1/1, 10:27 AM] yearqub: Haka kuma dan wasan na Portugal bai lashe kyautar dan wasan da ya taka rawa a gasar kofin duniya da aka yi a Rasha ba, ita ma Modric ne zakara.
Ronaldo ya lashe kofin Zakaraun Turai tare da Real Madrid, bayan da ta yi nasara a kan Liverpool da ci 3-1 a ranar 26 ga watan Mayun 2018.
Juventus tana ta daya a kan teburin Serie A, sannan ta kai zagaye na biyu a gasar cin kofin Zakarun Turai ta Champions League.
Haka kuma tawagar kwallon kafar Portugal ta kai wasan daf da karshe a Nations League, inda za ta fafata da Switzerland a cikin watan Yunin 2019 inda muka dosa.
DALILIN DAYA SA BA'A BINNE MARIGAYE SHEHU SHAGARI BA
Shi Marigayi Shehu Shagari ya rasu ne a ranar Juma'a a 28 ga watan Disamba a wani asibiti da ke babban birnin tarayya Abuja yana da shekaru 93. An binne shi ne kuma a wani kangon daki da ke wani sashen na gidansa da ke garin Shagari ranar Assabar. Mutane da dama sun yi tsammanin za a binne shi ne a Hubbaren Shehu inda kabarin Sheikh Usmanu Danfodiyo da na yawancin sarakunan daular Usmaniyya suke ciki.
HUJJAR KANNYWOOD; AN SAMU SABANI TSAKANIN NAFISA ABDULLAHI DA HADIZA GABON
Kannywood ta samu cewa duk da dai ba ta amsa tambaya game da dalilin da ya janyo sabani tsakaninsu ba a cikin firar, amma ta ce abu ne da ya faru kusan shekara daya da rabi, kuma ya riga ya wuce. "Ba ni son sake dauko wannan zancen." A shekarar 2017 ne fitattun jaruman guda biyu suka yi fada inda wasu rahotanni suka ce har da duka yayin da suke tsakar shirya wani fim. Nafisa ta ce babu wata dangantaka tsakaninta da Hadiza Gabon, bayan an tambaye ta ko suna kiran juna a waya. "Ba mu cika haduwa da Hadiza Gabon ba, idan mun hadu muna dan gaisawa da juna.
TABBAS NA CIKA DUKKAN ALKAWURRAN DANA DAUKA A ZABEN 2015 DA YA GABATA
Fadar Buhari, al’ummar Najeriya ba za su yi nadamar kada kuri’unsu ga ‘yan takarar jami’yyar APC a zaben 2019 da ke tafe ba. Shugaban ya ce, ya cika alkawuransa a bangarorin da suka shafi tsaro da tattalin arziki da kuma yaki da cin hanci da rashawa, yayin da ya jaddada aniyarsa ta ci gaba da sa kafar wando daya da masu wawure dukiyar talakawa muddin ya koma kan karagar mulki. Koda yake Buharin ya ce, yaki da mayakan Boko Haram na ci gaba da zama kalubale a wasu sassan kasar, amma za a kawar da matsalar tsaron da kungiyar ke haifarwa a kasar. Har ila yau, Buhari ya ce, matsalar rashin aikin yi na ci gaba da addabar kasar, amma gwamnatin na kokarin shawo kanta. A bangaren harkar noma kuwa, shugaba Buhari ya ce, gwamnatinsa ta karfafa guiwar manoma don tabbatar da tsaron abinci a fadin kasar baki daya.
Subscribe to:
Posts (Atom)