Sunday, 6 January 2019

AISHA BUHARI TAYI MAGANA AKAN GANDUJE A TARONTA NA KANO

   
   Uwar gidan shugaban kasar Najeriya Aisha Buhari a ranar Asabar din da ta gabata wajen taron da ta gudanar a jihar Kano ta kunyata Gwamnan jihar Dakta Abdullahi Umar Ganduje lokacin da ta tashi tayi tafiyar ta yana tsakar yin jawabin sa wajen taron. Kamar dai yadda muka samu, uwar gidan shugaban kasar ta gudanar da wani taro ne ta kungiyar ta ta yakin neman sake zaben mijin ta karo na biyu da ta kunshi mata da matasa tare da kaddamar da shugabannin ta a jihar.
     
      Kamar dai yadda jaridar DailyNigerian ta ruwaito, wannan ya sabawa al'ada kuma hakan bai rasa nasaba da irin yadda ba'a tsara jadawalin taron ba yadda ya kamata wanda hakan bai yi wa uwargidan shugaban kasar dadi ba.

AN KONA SHAGUNA DA GIDAJE A IBADAN


 Wasu batagari daga wasu sassan garin Ibadan, babban birnin jihar Oyo, sun saka wa gidaje fiye da 20 wuta a wani rikici tsakanin kungiyoyin 'yan daba a yankin Idi Arera. Daga cikin gine-ginen da 'yan dabar suka saka wa wutar akwai shagunan masu dinki, shagunan sayar da lemukan roba, shagunan kayan wutar lantarki da na abinci da na kayan sawa da sauran su. Majiyar ta shaida mata cewar barkewar rikicin na safiyar yau, Lahadi, ya biyo bayan rigingimun dake faruwa ne tsakanin kungiyoyin 'yan dabar. Rahotanni sun bayyana cewar ba don dagewar 'yan kungiyar bijilanti da wasu jama'ar unguwa ba yayin rikicin, da barnar da 'yan dabar zasu yi sai ta fi haka. A wani labarin na daga jihar ta Oyo, kun ji cewar Tsohon Sanata kuma tsohon gwamnan jihar, Rashidi Ladoja, ya ce ya yi ritaya daga yin takarar kowacce kujera a Najeriya saboda wahalar da ya ce ya sha lokacin da yake gwamna.

 sun kona gidaje da shaguna a sabon rikicin da ya barke a Ibadan  mai rike da mukamin Olubadan na kasar Ibadan, ya zama gwamna a jihar Oyo a tsakanin shekarar 2003 zuwa shekarar 2007 a karkashin jam'iyyar PDP. an tsige shi a watan Janairu na shekarar 2006, amma kotu ta mayar da shi a shekarar a watan Disamba na shekarar.
 
   koda yake wannan kalami a yau, Asabar, Ladoja ya bayyana cewar ya yanke shawarar yin bankwana da takara ne saboda samun lokacin kulawa da bukatun iyalinsa. A hirar sa da manema labarai a garin Igholo, hedkwatar karamar hukumar Oorelope, Ladoja ya ce, "kadan ya rage na manta da iyalina lokacin da nake gwamnati. Mun yi iya bakin kokarinmu, amma ni kam ba zan kara yin takara ba.

Thursday, 3 January 2019

FADAR JARUMAR HAUSA FILM MAI SUNA NAFISA ABDULLAHI AKAN ADAM A ZANGO


  Hakika Shahararriyar jarumar na ta masana’antar shirya fina-finan Hausa wato Kannywood Nafisa Abdullahi ta bayyana matsayar soyayyarta da jarumi Adam A. Zango, a cewarta a baya sun yi soyayya da shi, sai dai yanzu mutunci ne kawai tsakaninsu, amma ba soyayya ba. A shekarun baya an yi tunanin Nafisa Abdullahi da Adam za su yi aure duba ga yadda suka fito karara suka nuna suna matukar kaunar juna.
 
   to Amma Jarumar ta ce yanzu tsawon shekara biyar ba su tare. Ta ce kamar yadda Allah Ya hada su kuma Ya raba. Nafisa ta ce: "Ba sai na fito na fara bayanin an yi kaza ko kaza ba, zama ne ya zo karshe muka rabu," in ji Nafisa bayan an tambaye ta dalilin rabuwarsu. "A baya mun fi ayyuka tare kuma an fi ganinmu tare amma yanzu ba mu cika haduwa da juna ba sosai saboda ban cika fitowa a fina-finai ba.

   ita Jarumar ta ce yanzu ta dauki Zango a matsayin abokin aiki amma ba soyayya tsakaninsu. Ta ce ba su cika haduwa da shi ba a yanzu. "Ba mu da wata matsala ta rashin jituwa da juna tsakani na da shi.

SABANIN RA.AYIN 'YAN FINAFINAI AKAN SHUWAGABANCIN NAJERIYA

Ta yayin da siyasa ke cigaba da mamaya da ratsa jiki da harkokin jama'a, an yi sharhi a kan yadda goyon bayan Atiku da Buhari ya raba kan jaruman Kannywood

- Yin sharhin ya biyo bayan ganin yadda jaruman ke fitowa fili domin nuna goyon bayansu ga dan takarar da su ke ra'ayi

- Sai dai har yanzu ba a san ina wasu fitattun jarumai irin su Ali Nuhu, Sadiq Sani Sadiq, Rahama Sadu, Hadiza Gabon da Nafisa Abdullahi su ka saka gaba ba

Masana'antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood ta bawa shugaba Buhari muhimmiyar gudunmawa wajen samun nasara a zaben shekarar 2015.

Jaruman fina-finan Hausa da mawaka sun sha halartar taron jam'iyyar APC da yakin zaben Buhari domin nuna goyon bayansu. Kazalika mawaka sun rera ma sa wakoki.
[1/3, 4:22 PM] yearqub: akasarin jaruman sun kasance suna goyon bayan buhari sai dai yanzu fitowar Atiku a PDP ta janye wasu jaruman fina-finan.

Daga cikin jaruman Kannywood da har yanzu ke tare da Buhari akwai;

1. Adam A. Zango

2. Nura Hussain

3. Yusuf Haruna (Baban Chinedu)

4. Jamila Nagudu

5. Halima Atete

6. Rukayya Dawayya

7. Bello Muhammad Bello (BMB)

8. Dauda Kahutu Rarara (Mawaki)

DUBA WANNAN: Jerin sunayen jaruman Kannywood 12 da ke yiwa Atiku kamfen

9. Nazifi Asnanic (Mawaki)

10. El-Mu'az Birniwa (Mawaki)

11. Fati Nijar (Mawakiya)

12. Mawaki Aminu Ladan (ALA)

13. Hussaini Danko (Mawaki)

14. Fati Shu'uma

15. Rabi'u Rikadawa

Ragowar jarumar fim din Hausa irinsu Ali Nuhu, Rahama Sadau, Hadiza, Sadiq Sani Sadiq, Nafisa Abdullahi, da sauransu ba su bayyana dan takarar da su ke goyon baya ba.


CEWAR DAN WASAN REAL MADRID MAI SUNA ISCO


Hakika Dan wasan Real Madrid wato Isco yace bazai bar kungiyar a wasannan kakar wasannin ba, Dan wasan dai ana alakantashi da komawa kungiyar kwallon kafa ta Chelsea dake kasar England.

Manchester City suna neman dan wasan Real Betis mai suna Junior Firpo dan asalin kasar Spain mai shekaru 22.

Dan wasan Liverpool wato Solanke yana Crystal Palace ana gwajin lafiyarsa biyo bayan cimma yarjejeniya da Liverpool tayi da Crystal Palace kan daukan dan wasan a  matsayi na aro zuwa gaba.

ANTANTANCE HIJIRAN DAN WASAN B/DORMOUND MAI SUNA PULISIC


antantance dan wasan Dortmund wato Pulisic zai koma Chelsea ne ba Liverpool ba kamar yadda ake ta rade-radi.

Dan wasan da Barcelona, Manchester City da kuma Arsenal suke neman wato Nicolas Pepe ya shaidawa kungiyarsa ta Lille dake kasar France cewar shifa yanaso ya tafi.

TSOHON GWAMNAN KANO MAI SUNA AVM HAMZA ABDULLAHI YA RASU

lallai Labarin da muka samu yanzunnan na nuna cewa Allah ya yiwa tsohon gwamnan jihar Kano kuma tsohon ministan birnin tarayya, AVM Hamza Abdullahi rasuwa. Tsohon sojan ya rasu ne a kasar Jamus ranan Laraba, 2 ga watan Junairu, 2018. AVM Hamza Abdullahi ya kasance gwamnan mulkin soja ne tsakanin shekarar 1984 da 1985 yayinda shugaba Muhammadu Buhari ke mulkin kasar Nigeriarmu.